1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar G20 a taron WTO

December 13, 2005

Kungiyar kasashe masu tasowa ta G20 ta baiyana bukatun ta a taron ciniki na WTO

https://p.dw.com/p/BvSH
Shugaban hukumar WTO, Pascal Lamy
Shugaban hukumar WTO, Pascal LamyHoto: AP

Kungiyar nan da ta kunshi kasashe masu tasowa dake iran kanta, kungiyar G20, yanzu dai shekaru biyu da rabi kenan da kafa ta. Duk da haka, kungiyar ita ce ta biyu a jerin kungiyoyin da suka fi muhimmanci a hukumar ciniki ta duniya, wato WTO, bayan kungiyar hadin kann Turai. Kungiyar ta G20, ta kunshi mafi yawan kasashe ne dake kann hanyar samun ci gaban masana’antu, wadanda suka hada har da Brazil, China, India, Afrika ta kudu da Thailand. Sai dai kuma kungiyar ta kunshi kasashe ashirin da daya ne a cikin ta, maimakon kasashe ashirin kamar yadda sunan ta ya nuna.

To a wata sanarwa game da taron hukumar ciniki ta duniya, kungiyar G20 tayi kira ga Amerika da kungiyar hadin kann Turai su ci gaba da kyale kasuwannin su a bude domin shigar da kayaiyakin amfanin gona daga kasashe masu tasowa. Tun a lokacin taron baya da aka yi na WTO a Cancun shekaru biyu da suka wuce, kungiyar ta G20, ta tabbatar da ganin shawarwarin da aka yi basu sami nasara ba, saboda ta kasa samun nasarar jan hankalin kungiyar hadin kann Turai ta cimma bukatun ta. Daga cikin sauran kasashen kungiyar har da Masar da Argentina da Bolivia da Chile da Guatemala da Indonesia. Sauran kuma sune Cuba, Mexico, Nijeriya, Pakistan, Paraguay, Philipines, Zimbabwe da Tanzania da Uruguay da Venezuela.

Ministan ciniki na India, Kamal Nath yana ganin cewar babu sauran shakka a game da dalilan da suka sanya kasar sa ta shiga kungiyar ta G20. Yace:

Kasashen mu sun hade kansu karkashin inuwa guda ne domin su tabbatar da ana jin muryoyin su, saboda babu shakka an sami raguwar maida hankali kann bangaren raya kasa a shawarwarin dake gudana yanzu.

A hakika kuwa, shawarwarin Doha da aka kaddamar dasu shekaru hudu da suka wuce, an tanade su ne a matsayin shawarwarin shimfida hanyoyin taimakon raya kasa. To amma kasashe dake kann hanyar samun ci gaban masana’antu, kamar Brazil da Argentina da India da Afrika ta kudu da China, nan da nan suka lura da cewar ba zasu cimma burin su na samun karin damar shiga kasuwannin kasashen Turai ba. Saboda haka suka hade kansu karkashin kungiyar da suka kira, G20.

Wannan dai kungiya ce mai karfi. Kasashen cikin ta gaba daya suna da fiye da rabin yawan al’ummar duniya baki daya, kuma sune masu sayar da kashi daya cikin kashi hudu na kayan amfanin gona a duniya baki daya. Brazil alal misali, ita ce kasar da tafi sayar da waken soya da naman shanu da sukari a duniya. Sauran wakilai na kungiyar suna da irin wnanan sha’awa ta fadada cinikin su, saboda haka ma suke son ganin an sami sakamakon da ya dace a zauren taron Hongkong. Ministan ciniki na India, Kamal Nath yace:

Bama bukatar ganin taron na Hongkong ya zama dandali na jawabai da baiyana fatan alheri kawai. Wajibi ne a cimma wani abu na azo a gani a zahiri. Jawabai na fatan alheri da baiyana niyyar aikata wani abu, ba tun yau muka saba jin su ba, a duk lokacin da aka shirya irin wnanan taro.

Daga cikin matakan da kungiyar G20 take bukatar ganin an cimma wani sakamako na kirki a kansu, har da batun cinikin kayan amfanin gona, kamar yadda ministan harkokin wajen Brazil, Celso Amorim ya nunar a taron na Hongkong. Amorim, shine ya zama kamar jagoran shawarwari a madadin kungiyar G20, kuma shi da kwamishinan ciniki na kungiyar hadin kann Turai, Peter Mandelson, ana daukar su a matsayin wadanda suka fi angizo da muhimmanci a zaren taron na Hongkong.

Ministan harkokin wajen na Brazil yace cinikin kayan amfanin gona shine jigon shawarwarin na yanzu. Ci gaban da za’a samu ta wnanan fuska, shine zai zama ma’aunin nasarar da za’a samu a kokarin kammala shawarwarin tare da cikakkiyar yarjejeniya a shekara mai zuwa.

Haka kuwa yana nufin: sai idan kungiyar hadin kann Turai ta yi gyara a tayin da ta gabatar a bangaren cinikin kayan amfanin gona ne ita uma kungiyar G20 zata yi sassauci a daya bangaren shawarwarin: wato kyale kayaiyakin masana’antu daga kasashe masu ci gaba su shiga kasuwannin kasashe masu tasowa. Ministan ciniki na India, Kamal Nath yace ko da shike ba’a zaton wani abin kirki zai samu daga taron na Hongkong, amma kungiyar kasashen G20 suna sa ran zasu sami sabon tayi mai armashi daga kasashe masu ci gaban masan’antu. Idan kuwa ba haka ba, to kuwa babu wani ci gaba da za’a samu a shawarwarin Doha dake gudana a yanzu.