1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Al-Qaida a Yemen na habaka

August 7, 2013

Reshen Al-Qaida a kasashen Larabawa na da karfi musamman a Yemen, inda take amfani da rudanin da kasar ke ciki tana shirya hare-haren ta'addanci.

https://p.dw.com/p/19Lgs
Yemeni soldiers stand guard outside the German embassy as Yemeni demonstrators protest against the kidnapping of nine foreigners and the killing of three in north-western Yemen, in the capital Sana?a, Yemen, 29 June 2009. Hundreds of Yemenis took to the street in Sana?a to denounce the kidnapping of a German family of five and British engineer who were taken at gunpoint along with two German theology students and a South Korean teacher while on a weekend excursion in the restive Yemeni province of Saada. The bodies of the two German female students and the South Korean teacher were found in Saada three days after the kidnapping. The fate of the German family and the British engineer is still unknown as army and security forces continue combing vast mountainous and desert areas in northern Yemen. EPA/YAHYA ARHAB +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Da kamata yayi tun a ranar Talata, Tarayyar Jamus ta sake bude ofishin jakadancinta a birnin Sanaa na kasar Yemen, amma harabobin wakilan na Jamus za su ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa wani lokaci da ba a bayyana ba. Jamus dai ta dauki wannan mataki ne na rufe ofishin jakadancin nata bayan gargadin da Amirka ta yi cewa 'yan ta'adda na shirin kai hare-hare a kan cibiyoyin kasashen yamma dake a wasu kasashen Larabawa da na yankin Gabas ta Tsakiya, musamman a kasar Yemen.

A wani mataki na rigakafi Amirka ta rufe ofisoshin jakadancinta 22 a arewacin Afirka da kuma yankin Gabas ta Tsakiya. Barazanar kai wa 'yan kasashen yamman hari ta fi girma a kasar Yemen inda yanzu haka Amirka da Birtaniya sun kwashe 'yan kasashensu daga wannan kasa. Gargadin game da harin ta'addancin ya zo ne baya da hukumomin Amirka suka ce sun tari wata hira ta waya tsakanin shugaban Al-Qaida Aiman al-Zawahiri da shugaban Al-Qaida a yankin tsibirin Larabawa Nasser al-Wuhaischi. Reshen kungiyar Al-Qaida a kasashen Larabawa na da karfi musamman a Yemen, inda take amfani da rudanin da kasar ke ciki tana shirya hare-haren ta'addanci. Kasar ta kuma kasance wata tungar 'yan ta'adda. Sai dai a cewar Günter Meyer na cibiyar nazarin kasashen Larabawa ita ma kungiyar Al-Qaida a Yemen ta yi rauni.

"Gabanin watanni 18 da suka wuce Al-Qaida ta yi karfi a kudancin Yemen inda ta kwace yankuna da dama. Amma yanzu sun yi rauni saboda hare-haren jiragen saman yakin Amirka marasa matuka kai kaiwa tare da taimakon sojojin Yemen. Sai dai a hannu daya muna iya cewa karkashin shugabancin Nasser al-Wuhaischi, Al-Qaida a yankin ta ci gaba da kasance babbar barazana ga kasashen duniya."

FILE - An undated handout image made available by a Jihadist website on 24 February 2010, shows the senior leader of al-Qaeda in the Arabian Peninsula (AQAP) Nasser al-Wahaishi appearing in an Islamist video posted on internet. The U.S. has become increasingly worried about militants based in Yemen since al-Qaida groups there and in Saudi Arabia merged to become al-Qaida in the Arabian Peninsula. EPA/JIHADIST WEBSITE/HANDOUT BEST QUALITY AVAILABLE EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Al-Wuhaischi, mai shirya kai hare-hare

Shi dai Nasser al-Wuhaischi ya taba zama sakataren Osama bin Laden a Afghanistan. A shekarar 2001 ya tsere zuwa Iran, amma a 2003 an mika shi ga hukumomin Yemen wadanda suka tsare shi. Sai dai a 2006 yana daga cikin firsinonin da suka gudu daga wani kurkuku dake birnin Sanaa. Saboda alakarsa da Osama bin Laden an ba shi damar taka rawa cikin shugabancin reshen Al-Qaida, dake zama hadaka tsakanin 'yan ta'addan kasashen Saudiya da Yemen wadanda kuma suka addabi kasar Yemen da hare-haren. Kungiyar ce ake zargi da ba da horo ga dan Najeriyar nan Omar Faruk Abdulmutallab wanda ya so ta da bam a cikin wani jirgin saman a Amirka a shekarar 2009.

Yanzu haka ana tabka mahawara a Amirka ko za a iya girke sojojin kasar don ba da cikakkiyar ga ofisoshin jakadancin kasar a kasashen Larabawa. Sai dai Philipp Mißfelder kakakin jam'iyun CDU da CSU a kan manufofin ketare, ya ce wannan ba shawara ce mai kyau ba.

A fire truck extinguishes a blaze following an accidental explosion at an army ammunition depot in the Yemeni capital of Sanaa on October 18, 2012. According to a military source, a rocket fired during an army training session hit the warehouse by mistake. AFP PHOTO/MOHAMMAD HUWAIS (Photo credit should read MOHAMMED HUWAIS/AFP/Getty Images)
Hoto: MOHAMMED HUWAIS/AFP/Getty Images

"Wajibi ne a ba da muhimmanci ga ba wa ofisoshin jakadancin kariya, amma samar musu da wata rundunar kansu ba alheri ba ne."

Zagayowar ranakun kai hare-hare

Bisa bayanan da suka shiga hannun dan siyasar na Jamus dai, masana na kyautata zaton cewa an shiga wata gwagwarmayar rike madafun iko a cikin kungiyar Al-Qaida kan wanda zai yi nasarar kai mummunan hari a kan kasashen yamma a cikin makonni masu zuwa a daidai lokacin zagayowar shekara guda da kai hari kan karamin ofishin jakadancin Amirka a birnin Bengazin Libya da kuma zagayowar ranar hare-haren 11 ga watan Satumban shekarar 2001 a Amirka.

Mawallafa: Diana Hodali / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourrahmane Hassane

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani