1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Masar ta wanke Mubarak daga zargi

Mouhamadou Awal BalarabeNovember 29, 2014

Kotu ta ce Hosni Mubarak ba shi da hannu a cin hanci da karbar rashawa da kuma kashe-kashen da suka wakana lokacin juyin juya hali a shekara ta 2011.

https://p.dw.com/p/1Dx0c
Hoto: Reuters/A. Waguih

Wata kotun kasar Masar ta wanke hambararren shugaba Hosni Mubarak da 'ya'yansa biyu da kuma mukarrabansa daga ilahirin tuhume-tuhume da ake musu. An dai zargesu da laifin cin hanci da karbar rashawa tare da mara hannu a kashe-kashe masu zanga-zanga a lokacin da guguwar neman sauyi ta kada a Masar a shekara ta 2011.

Sai dai kuma tsohon shugaban na Masar da ya shafe shekaru 30 a kan kujerar mulki zai ci gaba da zama a gidan yari, sakamakon yanke masa hukunci daurin shekaru uku da aka yi a baya, bayan da wata kotu ta sameshi da wani laifin na cin hanci da kuma karbar rashawa.

Masoyan bayan Hosni Mubarack sun ta nuna farin cikinsu tun a cikin kotu, yayin da dangin wadanda aka kashe a boren da ya kai ga kifar da gwamnatinsa suka yi ta koke-koke don nuna bakin cikinsu. Kimanin mutane 846 ne suka rasa rayukansu a Masar a tsawon kwanaki 18 da 'yan kasar suka shafe suna boren kin jinin gwamnati shekaru biyun da suka gabata. Sai dai kuma hambararren shugaban na Masar ya yi ta nanatawa cewar ba shi da hannu a wannan aika-aika.