An dage shirin zaben shugaban Aljeriya
June 2, 2019Kotun koli ta tsarin mulkin kasar Aljeriya a wannan Lahadi ta bayyana cewa abu ne da ba zai yiwu ba a gudanar da zaben da zai maye gurbin Shugaba Abdelaziz Bouteflika kamar yadda aka tsara yi a ranar hudu ga watan Yuli mai zuwa.
A cikin wata sanarwa da kotun tsarin mulkin ta fitar a Lahadin nan, ta ce yanzu ya rage ga shugaban rikon kwarya Abdelkader Bensalah ya sa wata sabuwar rana da za a gudanar da zaben kasancewar biyu cikin 'yan takarar ma ba a tantance su ba.
Gangamin adawa dai da gwamnatin Shugaba Bouteflika ya sa ya sauka daga mulki a watan Afrilu bayan shekaru 20.
Tun dai a watan Fabrauiru ne dubban al'ummar Aljeriya suka tattaru a birnin Algiers da wasu birane don yin babban gangami na adawa da takarar Bouteflika a zaben da aka tsara yi 18 ga watan Afrilu. Inda masu adawar ke cewa babu batu na neman mulki a wa'adi na biyar ga shugaban da aka zaba tun a shekarar 1999.