Kotun ICC za ta binciken cin zarafin dan Adam a Burundi
November 9, 2017Talla
Kotun ta ICC ta sanar da wannan mataki nata ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Alhamis inda ta ce binciken zai shafi laifukan da suka hada da na kisa da azabtarwa da fyade da dai sauran laifukan cin zarafin dan Adam da aka aikata a cikin kasar ta Burundi ko kuma wadanda 'yan asalin kasar suka aikata a wasu kasashen ketare.
Wasu alkalumma da kotun ta ICC ta wallafa sun nunar da cewa mutane akalla dubu da 200 suka halaka a yayin da wasu sama da dubu 400 suka shiga gudun hijira a cikin rikicin siyasar da ya barke a kasar ta Burundi a sakamakon tazarcen Shugaba Nkurunziza. A watan Oktoban da ya gabata ne dai kasar Burundi ta kasance kasa ta farko da ta fice daga kotun ta ICC a hakumance.