Kotun ICC ta Tuhumi Thomas Lubanga
March 14, 2012Babbar kotun duniya da ke hukumta mayan laifukan yaƙi ta sami tsohon jagoran ƙungiyar yan' tawaye ta FPLC force Patriotique Pour la Liberation de Congo Thomas Lubanga,da laifin yin amfani da ƙannanan yara a matsayin soji a yaƙin da aka yi na ƙabilanci a lordin Etui da ke a yankin arewa maso gabashin jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a shekarun 2002 da 2003.
Da ya ke yi magana a lokacin da ake gudanar da sharar da ya jagorantar a birnin Hague ,alƙalin mai gabatar da ƙara Adrian Fulfpord ya ce nan gaba za a baiyana hukumci dangane da laifin da ake tuhumar mista lubunga sannan kuma yaƙara da cewar ''ya ce zauran shara'a baki daya ya yanke wannan shawara ta tuhumar mista Lubanga akan waɗanan laifuka. Lubunga ɗan shekaru 51 da haifuwa wanda ke sanye da fara gariya da hula fara ya riƙa murmushi a lokacin da alƙalin kotun ta ke karanto laifufukan da aka tuhume shi da aikata.ƙungiyar kare hakin bil adama ta Human Rights Wacth ta ce wannan wani sako ne mai ƙarfi ga sauran masu manyan laifukan yaƙi wannan dai shine karo na farko da kotun ta ICC ta yanke hukumci tun da aka kafa ta a shekara ta 2003.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar