Kotun ECOWAS ta yi umarni a saki Bazoum
December 16, 2023Kotun ta bayyana dokoki tsarin mulkin kungiyar ta ECOWAS da kudirorin Majalisar Dinkin Duniya da duka suka nuna babban laifi ne a tsare mutum ba tare da tuhuma kan laifin da ake zarginsa da aikatawa ba.
Da yake yanke hukunci, mai shari'a Gbéri-Bè Ouattara ya bayyana cewa kowane dan Adama yana da iko ya wala a ko ina. Don haka sojojin sun tafka laifi da suke ci gaba da tsare Mohamed Bazoum. Lauyoyin da suka shigar da karar a madadinsa sun saurari hukuncin ne ta kafar sadarwa ta Internet. Tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar suke tsare da Bazoum Mohamed.
Karin Bayani:ECOWAS na kan bakanta a kan Nijar
Hukuncin kotun dai muhimmin ci gaba ne ga kungiyoyin da ke fafutukar kare hakin jama'a a Afrika da ma sauran sassan duniya.
A shari'ar da kotun kolin Najeriya ta yanke a kan karar da shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB Nnamdi Kanu ya shigar gabanta, Kotun ta jingine hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke cewa baya da laifin ta'adanci a kansa. Kotun kolin ta ce za'a ci gaba da shari'ar sa a kotu a saboda haka babu batun a sake shi.