1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu za ta sallami Gbagbo idan ba zai koma gida

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
February 1, 2019

Alkalai a kotun ICC, sun bayyana cewa za su amince da sallamar da kotun ta yi wa tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo da Charles Blé Goudé muddin za a hana tsohon shugaban komawa kasarsa.

https://p.dw.com/p/3CZy0
Kombibild - Charles Blé Goudé und Laurent Gbagbo

Tshohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo wanda kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta caza da aikata laifi a shekarun 2010 da 2011, alkalan kotun sun wanke shi daga zarge-zargen a ranar 15 ga watan Disamba, to amma kuma masu daukaka kara a kotun suka bukaci da a ci gaba dakatar da shi.

Alkalan kotun dai na da hurmin ci gaba da rike Gbagbo da Charles Ble Goude har izuwa ranar da za a sake sauraren karar da masu daukaka karar suka shigar ko kuma a'a, kana kuma alkalan kotun na iya sallamarsu ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Lauyoyin da ke kare Laurent Gbagbon na ci gaba da kalubalantar kotun da ke fatan sakin tsohon shugaban bisa sharadi, suna masu cewar da a sallame shi takwana.