1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a kashe mutumin da ya kashe Hanifa

Abdul-raheem Hassan
July 28, 2022

Kotu ta sami mutumin mai suna Abdulmalik Tanko da abokin shi da laifin kisan gilla kan dalibarsa mai suna Hanifa Abubakar, wacce ya sace don neman kudin fansa sannan ya kashe ta tare da binne gawarta.

https://p.dw.com/p/4EmtU
Hoto: Loredana Sangiuliano/SOPA Images via ZUMA Press Wire/picture alliance

Hukuncin Koton da ke birnin Kano a arewacin Najeriya, ya biyo bayan shari'a na tsawon watanni shida tun bayan faruwar lamarin a karshen shekarar 2021.

Kotun ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan Abdulmalik Tanko tabbatar da samun sa da laifin kashe dalibarsa Hanifa Abubakar mai shekaru biyar a duniya. A watan Disamban 2021 ne Abdulmalik ya yi garkuwa da Hanifa inda ya nemi a bisa kudin fansa masu yawa, daga baya ya kashe ta ya binne gawarta a wani kango. 

A watan Janairu na shekarar 2022, 'yan sandan jihar Kano suka gano gawar Hanifa bayan dogon bincike sakamakon kama shi da wasu abokansa da ya hada baki da su wajen sace yarinyar.