1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta yanke hukunci mai tsauri a Turkiyya

Zulaiha Abubakar
June 20, 2019

Kotu ta yanke wa mutane 151 da suka hada da manyan sojojin kasar hukuncin daurin rai da rai sakamakon samunsu da laifin yunkurin hambarar da gwamnatin shugaba Recep Tayyip Erdogan tun a shekara ta 2016.

https://p.dw.com/p/3KnJC
Türkei Unterstützer der Bewegung von Fethullah Gülen
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Suna

Daga cikin wadanda kasar ta jima tana zargi da yunkurin juyin mulkin har da malamin addinin Islama Fethullah Gülen wanda har yanzu yake zaune a kasar Amirka da kuma tsohon shugaban sojin saman kasar Akin Oztuk da Mehmet Disli 'dan uwan tsohon dan majalisa a jam'iyya mai mulkin kasar. Iyalan wadanada suka rasa rayukansu yayin yaunkurin hambarar da gwamnatin Erdogan sun kasance cikin alhani a lokacin da Alkali ya sanar da yanke wannan hukunci daurin rai da rai ga wadanda aka samu da laifi. An dai fara shari'ar wadannan mutane tun a shekara ta 2017 a kotun da ke gidan yarin Sincan da ke babban birnin kasar.