1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin zaben Kenya ya dauki hankalin jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar SB)(AH
September 9, 2022

Kotu ta tabbatar da zaben Kenya da haka ne jaridar Süddeutsche Zeitung bude labarin da ta wallafa mai taken "Babu shaidar magudin zabe. Ruto ya zama shugaban kasa".

https://p.dw.com/p/4GdVd
Manyan alkalan kotun kolin Kenya lokacin hukuncin zaben shugaban kasa
Kotun kolin Kenya lokacin hukuncin zaben shugaban kasaHoto: Monicah Mwangi/REUTERS

A duk fadin kasar, a cewar jaridar dubun dubatar mutane ne suka taru a safiyar Litinin na wannan mako mai karewa don jin sakamakon kamar dai sakamakon wani muhimmin gasar kwallon kafa ne. An watsa a kan manyan allunan talabijin da wuraren shakatawa, a yayin da miliyoyin mutane suka bibiyi shari'ar ta yanar gizo a wayar salula.

Kotun kotun kolin Kenya lokacin hukuncin zaben shugaban kasa
Kotun Kolin KenyaHoto: Yasuyoshi Chiba/AFP

Kotun kolin Kenya ta yanke hukunci kan zaben ranar 9 ga watan Agusta a ranar Litinin, kuma a ko'ina magoya bayan 'yan takarar shugaban kasar sun fuskanci juna kamar magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa biyu. A gefe guda na William Ruto, mataimakin shugaban kasa mai ci, a daya bangaren kuma, Raila Odinga, wanda ya zo na biyu, wanda ya fafata a zabuka biyar ba tare da yin nasara ba. A yanzu ya sake shan kaye da kashi 48.8 cikin dari inda Ruto ya samu kashi 50.5.

Haka dai lamarin ya kasance, kotun kolin kasar ba ta ga wani dalili na tabbatar da daukaka karar Odinga ba. Ya gabatar da bayanai da kuma hujjoji da ke zargin an yi magudi wajen kidayar kuri'u miliyan 15 din da aka kada. Magoya bayansa sun yi ikirarin cewa wasu daga Venezuela sun yi kutsa cikin na'urar hukumar zabe don sauya sakamakon da ya bai wa Ruto nasara. Alkalin da ta gabatar da hukuncin Martha Koome ta ce shaidun Odinga jita jita ne kawai.

Mali | Sojojin Jamus a garin Gao na kasar Mali
Sojojin Jamus a MaliHoto: photothek/picture alliance

Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhi taken "Wani sabon yanayi a Mali, Bamako na nuna niyyar yin sulhu". Ta ci gaba da cewa nan ba da jimawa ba za rundunar Bundeswehr za ta ci gaba da aiki a kasar Mali da ke yammacin Afirka. Bayan da aka shafe makonni na kin amincewa, a baya-bayan nan gwamnatin mulkin soji ta ba da damar sauya takaitattun ma'aikata tare da barin fiye da jami'an rundunar Bundeswehr sama da 100 su fice daga kasar.

A cewar Ulf Laessing na gidauniyar Konrad Adenauer Foundation da ke Bamako, akwai alamun sassuci a bangaren gwamnatin mulkin sojin Mali bayan wasu tattaunawa. Ya ce har yanzu dai akwai sauran batutuwan da ba a warware su ba, amma ana ci gaba da aikin karba-karba na ma’aikata. Ceto sojojin Mali 22 da suka samu raunuka a baya bayannan da dakarun Bundeswehr suka yi, watakila ya sa gwamnatin sojan kasar ta fahimci kimar aikin rundunar ta Jamus.

Sharhin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta a kan yiwuwar fara yin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro nan ba da jimawa ba, saboda sabon maganin rigakafi yana da tasiri sosai.

WHO tana Rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a Malawi
Rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a MalawiHoto: Jerome Delay/AP Photo/picture alliance

Jaridar ta ce, idan mai binciken maganin alurar rigakafin Oxford Adrian Hill yana da hanyarsa, za a iya ba da lasisin rigakafin farko na rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a farkon shekara mai zuwa. A ranar Alhamis, Hill da sauran tawagar masu bincike daga Birtaniya da Burkina Faso sun ba da sanarwar sabbin bayanai daga gwajin rigakafin.

A cewar bayanan, maganin, wanda ake kira R21, ya ba da kariyar kaso 80 daga cikin 100 ga yara da aka yi wa allurar rigakafin fiye da matasan da ke cikin rukunin masu gwaji, wadanda suka karbi maganin da ake bai wa wanda kare ya ciza idan aka kwatanta.