Kotu ta haramta kama Godwin Emefiele
January 1, 2023Ya dai kira sunan rashin lafiya, ya kuma sa kafa ya fice daga Najeriyar a bangaren gwamnan babban banki na kasar da ke ta shan dumi daga kowace kafa cikin kasar a halin yanzu. Kama daga jami'an tsaro ya zuwa 'yan dokarta dai kusan kowa na neman ganin Godwin Emeifele ruwa-a-jallo da nufin amsa jerin tambayoyin aiki.
To sai dai kuma wata kotu a Abuja ta kai dauki tare da ba da kariya kan gwamnan da ya zuwa yanzu ke kasar Amirka a wani abin da ke kama da kokarin neman tsira. Cikin wani umarnin da ta bayar dai kotun ta ce ta haramta duk wani cin zarafi balle kamun gwamnan da jami'an tsaron DSS ke zargi da ta'ammali da kudade na ta'adda.
Kama daga 'yan sandan damara da ma masu takama da fararen kaya dai, kotun karkashin jagorancin mai shari'a Maimuna Hassan, ta ce jami'an tsaron sun gaza samar da issasun shaidun da ke iya kaiwa ga tabbatar da kamen gwamnan babban bankin kasar. Hujjar kuma da a cewar kotun ta bai wa gwamnan 'yanci daga kamu har Mahdi.
Emeifele dai na zaman mutum na biyu cikin kasar da ke amfana daga 'yancin kamun da ke zaman ba sabun ba. Kuma a fadar Barrister Buhari Yusuf da ke zaman wani lauya mai zaman kansa a Abuja, alkalin kotun na dogaro ne da sashen doka a wajen yanke hukuncin da ke iya sauya da daman gaske.
Emeifelen dai ya shiga tsaka mai wahalar gaske tun bayan kaddamar da wasu sababbin manufofin kudin da ke shirin tasiri har cikin fagen siyasa na kasar. Ana dai kallon bakar siyasar da ke kadawa a kasar a halin yanzu da ruwa da tsaki da jefa gwamnan cikin jerin rigingimu da masu siyasa ta kasar.
Sabon 'yancin dai na shirin bai wa gwamnan karin karfin iya kaiwa ya zuwa adawa da bukatu na masu siyasar da ke ta neman dagun kafa wajen aiwatar da sababbin manufofi na kudin.