Switzerland ta daure tsohon ministan Gambiya
May 15, 2024Talla
Kotun hukunta man'yan laifuka ta kasar Switzerland, ta yanke wa tsohon ministan cikin gida na kasar Gambiya Ousman Sonko hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari. An sami Sanko mai shekaru 55 da laifin cin zarafin bil adama a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh tsakanin shekarun 2000 zuwa 2016..
Kotun ta ce za kuma a haramta wa Ousman Sonko shiga kasar Switzerland na tsawon shekaru 12 da zarar an yanke hukuncin, sannan za a tilasta masa biyan diyya ga mutanen da ya azabtar.