Kotu ta daure Olisa Metuh shekaru bakwai
February 25, 2020Talla
Mai shari'a Okon Abang na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya tabbatar da hukuncin akan Olisa Metuh bisa laifuka bakwai da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta tuhume shi da su.
An tuhumi Olisa Metuh da karbar tsabar kudi Naira mliyan 400 ta hanyoyin da basu kamata ba daga hannun mai baiwa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan tsaron kasa Sambo Dasuki.
Dasuki wanda shima ake tuhumarsa a wata shari'ar ta daban ana zarginsa da karkatar da akalar kudi Dala biliyan biyu na kudin sayen makamai domin yaki da Boko Haram.