Kotu ta amince da zaɓen shugaba Goodluck Jonathan
November 1, 2011A wani hukunci da zai yi tasiri ga makomar siyasar Najeriya, kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasar ta yi watsi da karar da jamiyyar CPC ta shigar wacce ta kalubalanci zaben shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan, to sai dai tuni jamiyyar CPC tace za ta daukaka kara.
Alkalin kotun saurarren karara zaben Najeriyar da ya kwashe kusan sa'o'i biyu yana karanta dalilin da suka sanya kotun watsi da karar da jamiyyar CPC ta gabatar mai shari'a Kumar Akas yace ɗaukacin shaidun da jam'iyyar CPC ta gabatar basu da tasirin da zasu sanya a soke zaben, domin kuwa a lokuta da dama an samu sabani a shaidu 47 da jamiyyar CPC ta gabatarwa kotun, musamman shaidun da shugaban jamiyyar Prince Tony Momoha da na sakatarenta Buba Galadima suka gabatar.
Jigo a jamiyyar CPC Malam Nasiru Elrufai yace ai an dade da kamala wannan sharia..
Da wannan hukunci kotun tace dalilan da suka gabatar ba su isa su lahanta zaben shugaban Najeriyar ba balle ma a soke shi, don haka zaben shugaba Goodluck Jonatahan halatacce ne.
Tuni dai lauyan jamiyyar CPC Ahmed Bello Muhamoud esq yace su dai kam ba su gamsu da shari'ar ba.
Wannan ya sanya tambayar lauyan jamiyar PDP Alex esq ko ya yaji da hukuncin da suka kare a kotu? inda ya bayyana gamsuwarsa da hukunci.
Sai dai shi kuwa sakateren jamiyyar CPC Injiniya Buba Galadaima ya soki hukuncin da aka yake, wanda ya yi watsi da ƙarar tasu.
Magoya bayan jamiyyar PDP dai sun kasance cike da murnan sakamakon wannan hukunci da kotun ta yanke a Abuja, saboda tabbatar da hallarcin zaben kamar yadda sakataren jamiyyar Farefsa Rufai Alkali ya bayyana.
Wannan hukunci dai zai kasance mai tasiri ga fagen siyasa da ma na shari'ar Najeriya, musamman tun daga dakatar da shugaban kotun kolin Najeriya da ke ci gaba da haifar da cece kuce, da ma takadama da rigingimun da suka biyo bayan zaben shugaban kasar, abinda ke ci gaba da bayyana matsayin demokurdiyyar kasar. A yanzu dai za'a sa ido a ga fafatawar da za'a yi idan har jamiyyar CPC ta daukaka kara zuwa kotun kolin kasar a kan wannan batun.
Mawallaf: Mouhamadou Awal/ Uwais Abubakar Idris
Edita: Usman Shehu Usman