Kotu ta amince da takarar Jonathan a 2015
December 16, 2014kotun koli ta tilasta janye karar da ke bukatar hana shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan shiga takara a zabukan kasar da za su gudana a shekara ta 2015. Sai dai kuma bata bayyana ko ya saba ka'ida ga shugaban kasar na sake tsayawa takara ba ko kuma a'a.
Jonathan da ya karbi mulki bayan rasuwar marigayi Umar Musa Yar Adua a shekarar 2010 ya na fuskantar kalubalen daukar rantsuwa har sau biyu da shirin yin ta uku, abin da zai zamo irinsa na farko a kasar. Sake zaben nasa dai, zai mai da shi shugaba na farko da zai share shekaru sama da tara yana mulki a kasar bisa tsarin demokaradiyar kasar mai wa'adi na shekaru hudu-hudu sau biyu.
Dr Umar Ardo da ya nemi kotun tsaida Jonathan din daga takarar ya ce tilasta musu aka yi su janye takarar. Abin da ya sanya lauyansa daukar matakin.