1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Kudu na son yin sulhu da Arewa

Gazali Abdou Tasawa
July 17, 2017

Koriya ta Kudu ta yi wa takwararta ta Arewa tayin hawa tebirin tattaunawa a wani yinkuri na neman rage tsama tsakaninsu musamman bayan da Koriya ta Arewa ta yi nasarar harba makami mai lizzami mai cin dogon zango. 

https://p.dw.com/p/2gdi8
Südkorea Kaesong Industriegebiet
Hoto: Reuters/K.Hong-Ji

Wannan tayin neman sulhu da Koriya ta Kudu ta yi shi ne na farko da kasar ta yi tun bayan hawan Shugaba Moon Jae-In kan karagar mulkin kasar a watan Mayun da ya gabata. Tuni ma dai ministan tsaro na Koriya ta Kudun ya bayar da shawarar gudanar da zaman tattaunawar a kauyen Panmunjon na kan iyakar kasashen biyu da ake yi wa lakabin kauyen tsagaita wuta. 

Ita ma dai daga nata bangare Kungiyar agajin kasa da kasa ta Redikuros ta yi tayin sake hada kasashen biyu kan tebirin tattaunawa da nufin sake farfado da tsarin nan na tarukan haduwar iyalan Koriyoyin biyu wadanda suka kasance a rabe tun byan yakin da kasashen biyu suka gobza a shekara ta 1950 zuwa 1953.