1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kim na shirin sulhu da Koriya ta Kudu

Abdul-raheem Hassan
September 30, 2021

Shugaba Kim Jong Un ya nuna sha'awar sake farafdo da layukan sadarwa da suka tsaya cik tsakanin kasarsa da Koriya ta Kudu, Shugaba Kim ya yi tsokaci ne a gaban majalisar Koli na kasar.

https://p.dw.com/p/414BE
Nordkorea I Kim Jong Un
Hoto: Korean Central News Agency/Korea News Service/AP/picture alliance

A watan Agusta ne gwamnatin Pyongyang ta yanke layin sadarwa tsakaninta da Koriya ta Kudu, bayan atisayen soji na hadin gwiwa tsakanin Koriya ta Kudu da kasar Amirka.

Ana dai ganin Koriya ta Arewa na shirin sabunta hulda da makociyarta ta Koriya ta Kudu don samun sassaucin karayar tattalin arziki sakamakon takunkumin Amirka da sauran kasashen duniya.