1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kim Jong Un ya cilla makami mai linazami

Abdul-raheem Hassan
January 15, 2022

Gwamnatin Kim Jong Un, ta tabbatar da sake gwajin makamai masu linzami a wani mataki na mayar da martani kan takunkuman karya tattalin arziki da kasar Amirka ta sake sa mata.

https://p.dw.com/p/45ZOL
Koriya ta Arewa
Gwajin makami mai linzami a Koriya ta ArewaHoto: YONHAPNEWS AGENCY/picture alliance

Sabbin gwajin makamai masu linzamin da Pyanyong ta yi, na zuwa ne sao'i kalilan bayan gargadin da ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewar ta yi , na daukar mataki masu zafi kan gwamnatin Joe Biden idan ba ta sassauta takunkuman da ta sa ba.

Sai dai masana na ganin rashin jituwa tsakanin manyan kasashen biyu, na cigba da haifar da barazana ga zamantakewa a yankin Koriya kamar yadda Farfesa Yang Moo-jin na jami'ar Koriya ta Arewa yake cewa "Wannan sabon gwajin, sako ne Koriya ta Arewa ke isarwa, cewa ba za ta yi watsi da aikinta na makamai masu linzami ba. Kuma martani ne na dakile takunkuman da Amirka ta sa mata, sai dai ramuwar gayyar da kasashen buiyu ke wa juna, ba abin da ke haifarwa sai tashin hankali a yankunan Koriya."