1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta soki manufar taimaka wa Ukraine

Ramatu Garba Baba
January 27, 2023

Koriya ta Arewa ta zargi Amirka da kara rura wutar yakin Gabashin Turai a sakamakon taimaka wa Ukraine da ta yi da makaman yaki da sunan kare kanta daga mamayar Rasha.

https://p.dw.com/p/4MoIz
Hoto: picture-alliance/Ulrich Baumgarten

A daidai lokacin da rahotannin ke cewa Rasha na kara zafafa hare-haren da ta ke kai wa a arewa da gabashin Ukraine, ita kuwa Koriya ta Arewa ta soki matakin Amirka na taimaka wa gwamnatin Kyiv da tankunan yaki da ta ce, taimakon ba zai yi tasiri ba illa ya kara rura wutar rikicin yakin da ke ci a gabashin Turai.

Kalaman na kanwar Shugaba Kim Jong Un, wato   Kim Yo Jong, sun tabbatar da zargin da aka jima ana yi wa Koriya ta Arewa na mara wa Rasha baya a mamayar Ukraine, dama wannan ba shi bane karon farko da kasar ke sukar Amirka da zama kanwa uwar gami a rikicin makwabtan biyu.

A daya bangaren, kasashen tarayyar Turai sun dauki mataki na tsawaita takunkumin karya tattalin arzikin da suka sanya wa Rasha da wasu karin watanni shida a taron da suka yi a wannan Jummar, takunkuman sun hadar da tazgaro ga hada-hadar mai da musayar kudade da wasu haramcin da suka shafi Shugaba Vladimir Putin kai tsaye.