SiyasaAsiya
Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami a karo na tara
March 5, 2022Talla
Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzamin da ba a kai ga tantance irinsa ba a ta fuskar gabashin tekun Koriya. Jami'an makwabciya Koriya ta Kudu da kasar Japan ne suka sanar da haka a wannan Asabar.
Duk da dandana tankunkuman karya tattalin arziki da kasashen duniya suka kakaba mata a kan mallakar makaman nukiliya, Koriya ta Arewa ta yi fatali da tayin Amurka na tattaunawa.
A shekara ta 2019, an rabu dutse a hannun riga a tattaunawar Shugaba Kim Jong-un da tsohon shugaban Amirka Donald Trump a game da makaman nukiliyar Koriya ta Arewa.