Koriya ta Arewa ta harba makami mai lizzami.
July 31, 2019.Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito wani na hannun daman shugaban hafsan sojan Koriya ta Kudu na cewa an harba makaman ne tun da sanhin safiyar wannan Laraba a wani wuri da ke kusa da birnin Wonsan da ke gabar ruwan gabashin Koriya ta Arewar, kuma sun yi tafiyar zangon kilomita 250 kafin sun fada a cikin tekun ta Japan.
Wanann na zuwa ne kwanaki shida bayan da Shugaban Koriya ta Arewar Kim Jong Un da kansa ya jagorancin harba wasu makaman masu lizzabi masu cin matsakaicin zango guda biyu da nufin nuna rashin amincewarsa da atisayen sojoji na hadin gwiwa da Koriya ta Kudu da Amirka ke shirin somawa a yankin.
Wadannan gwaje-gwaje na baya bayan nan na zama na farko tun bayan ganawar da Shugaba Kim ya yi da Donald Trump a watan Yunin da ya gabata da Koriya ta Arewa ta yi wani gwajin makami mai lizzami.