Koriya ta Arewa ta rusa tattaunawa da Amirka
February 21, 2018Talla
Mataimakin shugaban kasar Amirka Mike Pence ya shirya tsaf don tattaunawa da za ta kafa tarihi tsakanin Amirka da jami'ai na Koriya ta Arewa a lokacin wasannin hunturu na Olympic a Koriya ta Kudu sai dai katsaham gwamnatin Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ta rusa shirin tattaunawar ana daf da farawa kamar yadda Amirka ta bayyana a ranar Talata.
A cewar mahukuntan na Amirka dai mataimakin shugaban na Amirka Mike Pence ya shirya amfani da wannan dama don sanin mataki na gaba kan Koriya ta Arewan, sai dai yanzu wannan wata dama ce ga Amirka ta kara jajircewa wajen ganin mahukuntan na Pyongyang sun ajiye shirinsu na mallakar makamin nukiliya da manyan makamai masu linzami.