1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Koriya ta Arewa ta gargadi Amirka kan Nukiliya

June 22, 2021

Koriya ta Arewa ta gargadi Amirka da ta daina yi mata mummunar fassara a kan shirinta na Nukiliya, tana mai zargin Amirka da yin soki-burutsu domin cimma wata manufa.

https://p.dw.com/p/3vMib
Nordkorea Kim Jong Un
Hoto: KCNA/AP Photo/picture alliance

A sanarwar da Kim Yo Jong, wata babbar jigo a jam'iyya mai mulklin Koriyan kuma 'yar uwa ga Shugaban Kasar Kim Jong Un ta fitar ta zargi Mai ba Shugaban Amirka Shawara ta Fuskar Tsaro Jake Sullivan da yi wa Shugaba Kim mummunar fassara. 

An dai ruwaito Sullivan a ranar Lahadi na zargin shugaban Koriya ta Arewa da nuna wa Amirka d'agawa da kokari na nuna cewa a shirye yake da yaki, a daidai lokacin da yake cewa kasarsa za ta iya amfani da diflomasiyya wurin mu'amulla da Amirka.

Sai dai babbar jami'ar ta Koriya ta Arewa ta ce wannan ba gaskiya ba ne, Amirka na yin irin wannan fassara ne don kawai ta cimma wata manufarta kuma idan Amirka ta ci gaba da hakan to a karshe ita ce za ta ji haushi.

An dai kwashe shekaru masu yawa ana zaman doya da manja a tsakanin Amirka da Koriya ta Arewa dangane da makaman Nukiliyar Koriya ta Arewa wanda a yanzu Shugaba Joe Biden ke kokarin ganin Koriyan ta dakatar da mallakarsu.