Tsamin dangantaka a yankin Koriya
August 16, 2019Talla
Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta fara tsami ne bayan da shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa, ya zargi takwaransa shugaba Moon Jae-in na Koriya Kudu da yaudara sakamakon wani atisayen sojoji na hadin gwiwa tsakanin Amirka da Koriya ta Kudun.
Gabanin harba makaman sai da wakilan kwamitin sulhunta kasashen biyu daga bangaren shugaba Kim na Koriya ta Arewa suka jadadda aniyar kasar ta juya wa shirin inganta alaka tsakanin kasashen baya, wannan dai shi ne karo na shida cikin kankanin lokaci da Koriya ta Arewa ke harba irin wadannan makamai a ci-gaba yi wa makociyar ta ta gargadi.