1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta gayyaci Koriya ta Kudu

Yusuf Bala Nayaya MNA
February 10, 2018

Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya gayyaci takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-in don tattaunawa a birnin Pyongyang.

https://p.dw.com/p/2sRUE
Südkorea Seoul Treffen von Kim Yo Jong, Ri Son Gwon
Kim Yo Jong 'yar uwa ga shugaban Koriya ta Arewa na ganawa da abokin tafiyaHoto: picture alliance/AP/Yonhap/K. Ju-sung

Kamfanin dillancin labaran Yonhap na Koriya ta Kudu ya bayyana labarin gayyatar a wannan rana ta Asabar da ke zuwa bayan da jami'ai na gwamnatin Koriya ta Arewa suka je kasar ta Koriya ta Kudu don halartar bude bikin wasannin Olympics na lokacin hunturu a birnin Pyeongchang.

Shugaba Moon Jae-in na Koriya ta Kudu ya gana da manyan jami'ai daga Koriya ta Arewa ciki kuwa har da 'yar uwan shugaban kasar Koriya ta Arewa. Tuni ma dai suka kammala tattaunawar a wannan Asabar kamar yadda fadar shugaban ta nunar, sai dai babu karin haske kan abin da tattaunawar ta kunsa.