1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Koriya ta Arewa ta gargadi Amurka da kuma Koriya ta Kudu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 5, 2024

A cikin watan Janairun da ya gabata Koriya ta Arewa ta harba makamai zuwa iyakarta da makwabiciyarta ta Koriya ta kudu, lamarin da ya janyo zazzafan martani daga Koriya ta Kudu

https://p.dw.com/p/4dAT3
Hoto: YNA/picture alliance

Koriya ta Arewa ta ce Koriya ta Kudu da kuma Amurka za su dandana kudarsu sakamakon atisayen sojoji na hadin gwiwa na takalar fada da suka fara gudanarwa a makon nan da ke zama tamkar sharar fagen fara mamayar Koriya ta Arewa.

Karin bayani:Koriya ta Arewa na yin barazana ga Amirka

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin tsaron Koriya ta Arewa ta fitar a Talatar nan, ta ce gangamin atisayen sojojin kasashen biyu shiri ne na tunzura ta, tare da haddasa rincabewar lamuran tsaron yankin baki-daya, a don haka Pyongyang ba za ta saurara wa Seoul da Washington ba ko kadan.

karin bayani:Koriya ta Arewa za ta cigaba da kera nukiliya

A cikin watan Janairun da ya gabata Koriya ta Arewa ta harba makamai zuwa iyakarta da makwabiciyarta ta Koriya ta kudu, lamarin da ya janyo zazzafan martani daga shugaba Yoon Suk Yeol na Koriya ta Kudu da ke cewa a shirye suke su farwa Koriya ta Arewa da zarar ta kai musu hari.