1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake gwajin makaman Koriya ta Arewa

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 28, 2022

Koriya ta Arewa ta sake harba makamai ma su linzami guda biyu zuwa Tekun Gabashin Chaina, kwanaki biyu bayan wani gwajin makami mai linzami da ta yi.

https://p.dw.com/p/4HU8v
Koriya ta Arewa | Makamai ma su Linzami | Gwaji
Koriya ta Arewa dai, ta saba neman magana wajen yin gwajin makamai ma su linzamiHoto: Choo Sang-chul/Newsis via AP/picture alliance

Wannan sabon gwajin makaman dai, na zuwa ne gabanin ziyarar da mataimakiyar shugabar Amirka Kamala Harris za ta kai makwabaciyar Koriya ta Arewan kana abokiyar tagwaitakarta da kuma takun sakarta Koriya ta Kudu. Rundunar sojojin Koriya ta Kudun ta bayyana cewa, ta gano makamai masu linzami da ba sa cin dogon zango guda biyu da aka harba daga fadar Pyongyang. Rahotanni sun nunar da cewa an harba makami na biyu, mintuna 10 bayan harba na farko.