Koriya ta Arewa na son zantawa da Amirka
February 25, 2018Talla
Janar din mai suna Kim Yong Chol ya ambata hakan ne Pyeongchang na kasar Koriya ta Kudu gabannin rufe wasannin Olympics da aka yi a yau (25.02.2018), inda ya ke cewar Pyongyang na da kyakkyawar niyya ta tattauawa da Washington. Amirka da Koriya ta Arewa sun jima su na takun saka sai dai lamarin ya fi kamari tun bayan hawan Donald Trump kan gadon mulki inda ya kasance a sahun gaba na shugannin duniya da ke son ganin an matsawa Arewa din lamba don ta yi watsi da shirinta na kera makaman kare dangi.