Makami mai linzamin Koriya ta Arewa
January 6, 2022Talla
Kazalika wannan na kasancewa gwaji na biyu da kasar ta yi ikirarin yi da makaman ma su cin dogon zango bayan wanda ta yi a watan Satumbar bara, duk da takunkumai da kuma kushen da take fuskanta daga kasashen duniya. Ministan tsaro na kasar Japan Nobuo Kishi ya bayyana makaman da nau'in makami da Koriya ta Arewa ba ta taba harba irinsa a baya ba. Makami mai cin dogon zangon da Koriyan ta harba a wannan lokacin, na da saurin gaske kuma ya na gudu sau biyar fiye da wanda aka sani. Tuni dai kasashen Amirka da Japan da kuma Kanada, suka yi tir da gwajin na Larabar wannan makon.