1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici tsakanin gwamnati da 'yan tawaye ya tsananta a Yemen

Zulaiha Abubakar
August 30, 2019

Ministar harkokin kasashen ketare a Sweden Margot Wallström za ta kai ziyarar aiki yankin Gabas ta Tsakiya da nufin bude sabon babin tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin Yemen da 'yan tawayen Houthi.

https://p.dw.com/p/3Om8M
Margot Wallström
Hoto: picture-alliance/dpa

Ministar ta bayyana cewar za ta gayyaci jama'a da ga bangaren 'yan ba ruwanmu don sauraron shawarwarinsu kafin ta gana da wakilan Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin na kasar Yemen, daga cikin kasashen da minista Wallstrom za ta ziyarta akwai Saudiyya da Jordan da kuma kasar Oman.

A watan Disambar bara Majalisar Dinkin Dunyar ta jagoranci sulhunta bangarorin a wani zaman tattaunawa da birnin Stockholm na kasar ta Sweden kafin bangarorin dake rikici da juna su karya ka'idodin da aka cimma.  A wani sabon labarin kuma jami'an gwamnatin ta Yemen sun bayyana yadda wani sashe na 'yan tawayen masu ikirarin aware suka kai farmaki gidajen sojoji da kuma ma'aikatan gwamnati a birnin Aden.