Tafkin Chadi: Kokarin magance rikici
July 27, 2021An dai dauki wannan matakin ne, a kokarin magance matsalolin yankin ciki kuwa da har da matsalar rikicin Boko Haram. Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake cika shekaru 13 da fara rikicin Boko Haram a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, wanda ya bazu zuwa jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya da ma wasu sassan kasashen da ke bakin gabar Tafkin Chadin wanda har yanzu aka kasa magance shi. Yanzu haka dai hukumomin da ke kula da Tafkin Chadin sun fara shirin janyo ruwa da wasu koguna da su ka ratsa sassan nahiyar Afirka, domin farfado da wannan tafkin da ke zama tushen tattalin arzikin al'ummar yankin.
Karin Bayani: Mafita ga yankin Sahel da Tafkin Chadi
Al'ummar da ke bakin gabar sun ji dadin wannan labarin kamar yadda Alhaji Abubakar Gamandi shugaban kungiyar masu hada-hadar kifi a bakin gabar Tafkin Chadin ya bayyana. Masana Kamar Kwamarade Dauda Muhammad Gombe sun yi imanin cewa, in aka farfado da tafkin zai taimaka wajen samar da karin ayyukan yi ga matasa da ake ganin sune ake zawarcinsu suna shiga kungiyoyin 'yan ta'adda saboda rashin aikin yi.
Ra'ayoyin al'ummar da rikicin ya shafa sun bambanta, inda wasu ke bayyana cewa ana samun nasara wasu kuma na cewa da sauran aiki. Malam Abba Aji wani ma'aikacin jami'ar Maiduguri ya ce sun samu zaman lafiya, amma a cewar Shatima Abdullahi in ana samun nasara a wasu wurare akwai kuma inda har yanzu ana fama da matsalar.
Karin Bayani: Boko Haram na zafafa hare-hare a Nijar
Sai dai kwamnadan rundunar da ke yaki da 'yan ta'addan a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriyar da ake kira da "Operation Hadin Kai", Manjo Janar Christopher Musa ya ce suna da kwarin gwiwa an kusa kawo karshen wannan rikici. Al'ummar yankin dai na fatan hukumomi za su kara fito da hanyoyin da za a farfado da harkokin rayuwa da tattalin arzikin kasa da tsaro, ta yadda al'ummomin da su ka fara komawa garuruwasu za su samu karfin gwiwar zama domin farfado da yankunan.