kokarin sasanta rikicin siyasar Togo
May 18, 2005Hausawa dai kance waiwaye adon tafiya,wata kungiyyar kare hakkin bil adama a kasar Togo tace mutane 58 ne suka rasa rayukan su wasu kuma 317 suka jikkata sakamakon rikice rikicen da ake fuskanta a kasar kafin zaben shugaban kasa da kuma bayan sa.
Daga cikin wan nan kididdiga a cewar hukumar kare hakkin bil adaman 27 daga cikin jumlar yan jamiyyar RPT ne ta shugaba Faure Gnassingbe Eyadema goma sha uku daga jamiyyar adawa, guda takwas kuma jamian tsaro ne kana ragowar goman mutane ne daga kasashen Nigeria da Mali da kuma Niger.
A waje daya kuma a yayin da ake kokarin kafa gwamnatin hadaka a daya hannun kuma jamiyyun adawar kasar da alama na nan akan bakansu na cewa sai dai a sake kirga wadannan kuriu, don a cewar su an tafka magudi ne a lokacin kidayar data bawa Faure Eyadema nasara.
Duk da cewa kungiyyar Ecowas da kungiyyar hadin kanm kasashen Africa wato Au da kungiyyar gamayyar turai Eu da kuma kasar Amurka sun aminta da wan nan zabe daya bawa Faure Eyadema Nasara, har yanzu jamiyyun adawa na kasar basu amince da Mr Faure Gnassingbe Eyadema ba.
A misali kakakin jamiyyun adawa na kasar ta Togo wato Crosby Kuist yace a shirye suke su halarci taron kolin birnin na Abuja a gobe Alhamis amma bada sunan taron kolin kungiyyar Ecowas ba.
Kakakin yaci gaba da cewa koda bayan isar su Abuja sun gano cewa taron na kungiyyar Ecowas ne ba wanda Obasanjo ya kira ba, to babu makawa zasu dawo izuwa gida ba tare da wani bata lokaci ba.
Bayanan bayan fage dai sun shaidar da cewa wan nan taron kolin za a gudanar dashi ne karkashin laimar kungiyyar ta Ecowas bisa manufar tattauna matsalolin siyasar ta Togo tare da samo bakin zaren warware rikicin cikin ruwan sanyi ba tare da fadawa cikin wata sabuwar rigimar ba.