Kokarin sasanta rikicin kasar Yemen
September 12, 2014Manzon musamman na MDD a kasar ta Yemen, Jamal Bin Umar,wanda yakai gwauro yakai mari, tsakanin wakilan gwamnati a gefe daya, da kuma shuwagabannin kabilar Hauthiyeen da kungiyar Ansarulllah a daya gefen, yayi nasarar shawo kan bangarorin biyu su rattaba hannu kan yarjejeniyar sasantawar da MDD da kasashe Sarakunan Larabawan Gulp, zasu sa ido don ganin an aiwatar da ita. hugaban kasar ta Yemen, Abdurabbu Mansur Hadi, wanda ya amince da kafa sabuwar gwamnatin hadaka da za ta kunshi wani kaso na kungiyar Hauthiyeen a cikinta, da kuma dauke Karin da akaiwa makamashi, kamar yadda yarjejeniyar da ake shirin rattaba hannu kanta ta tanada,shugaban na Yemen, ya siffanta kawo karshen wannan dambaruwa da kwato kasar daga bakin kura.
Ita dai kasar ta Yemen, da a baya ta zama tungar yan kungiyar Alka'ida, wadanda Amirka ke farautarsu a kai a kai da jiragen yaki masu sarrafa kansu, ta kusan tsunduma yakin basasa a yan watannin nan, bayan da kabilar ta Hauthiyeen dake da dimbin mabiya, tayi hadin guiwa da magoya bayan tsohon shugaban kasar, Ali Abdallah Saleh, yadda suka kafa kawancen adawar dake neman ganin bayan gwamnati mai ci, kawancan da ke bin matakan lumana dana fito na fito da makamai don cimma manufarsa.