1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin neman sasanta rikicin PDP a Najeriya

Uwais Abubakar Idris M. Ahiwa
November 14, 2022

Ga dukkan alamu babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya na cikin fatan samun sulhu a rikicinta na cikin gida, bayan gwamnoni biyar da suka fusata sun sake nuna alamu na samun sulhu.

https://p.dw.com/p/4JVBe
Atiku Abubakar, dan takarar PDP a zaben Najeriya
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP

Alamun samun daidaito a babbar jam'iyyar ta adawa a Najeriya PDP ya fito ne bayan dan takarar neman shugabancin kasa na jam'iyyar Atiku Abubakar ya yi marhabin da tayin da gwamnonin biyar masu jayayya da takararsa karkasjin jagorancin gwamnan jihar River Nyesom Wike sun nuna cewa kofararsu a bude take na a sulhunta.

Kokari na sasanta rigingimun cikin gida da suka sanya jam'iyyar ta PDP darewa gida biyu a kan takarar Atiku Abubakar din lamari ne da ke jan hankalin 'ya'yan jam'iyyar manya da kanana. Abin da ya sanya hanzari na maraba da wannan tayi da gwamnan jihar Rivesr Nyesom Wike ya yi, wanda ya zama madugu uban tafiya na gwamnaonin biyar na jam'iyyar da ke hura wutar rikici a cikin PDP.

Gwamna Nyesom Wike, jigo a PDP
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Da alamun Gwamna Wike ya kama hanyar lashe aman da ya yi a kan wannan batu da a baya ya dage ba za su fita daga jam'iyyar kuma ba za su hakura da bukatunsu ba. Amma tuni dai dan takarar neman shugabancin Najeriyar a PDP Atiku Abubakar ya bayyana mrahabin da wannan tayi. Su dai gwamnonin biyar sun dage a kan sai a sauke shugaban jam'iyyara Iyorchia Ayu daga mukaminsa.

To sai dai, sanin yadda yanayin siyasa yake musamman a daidai lokacin da ake fuskantar babban zabe na shugaban kasa, ra'ayoyi na shan bamban a kan wannan zumudin da tayin da Wiken ya yi, sanin a baya sai an yi kamar za a shirya, amma kuma sai gayyar ta watse.

Ita dai uwar jam'iyyar PDP na cike ne da fata, musamman ma shi dan takarar neman shugaban kasarta su samu sulhu da gwamnonin biyar duk da rashin tabbas da ke tattare da lamarin, a daidai lokacin da take tunkarar babban zabe a Najeriyar ganin irin sanin da ta yi wa hadarin da rikicin cikin gida ke da shi gare ta a matsayinta na jam'iyyar mai adawa a kasar.