Kokarin dinke baraka a cikin PDP
January 27, 2014A wani abun da ke zaman yunkurinsa na sake maido da tarwatsatsen garken PDP, sabon shugaban jam'iyyar na kasa ya fara zagaye ga 'yan tawayen da ko dai suka bar jam'iyyar ko kuma suka je hutun dole da nufin nuna bacin ransu da halin da gidan na wadata ya samu kansa ciki tsundum.
Ya dai ga karin kumallo da 'yan biyar na PDP da suka yi sauyin sheka suka koma APC, kamun daga baya ya gana da daya a cikin biyun da ya ce babu gudu babu ja da baya cikin jam'iyyar, sannan sai babban dodo na ukun da ya ce ya tafi hutun dole, duk dai a kokari na sauyin ra'ayi ga shugaban jam'iyyar PDP dake nuna alamar sulhunta tsakanin 'ya'yan jam'iyyar cikin kankanen lokaci.
Kyakkyawan fata a cikin PDP
Duk da cewar dai har ya zuwa yanzu babu sakamakon koda guda cikin ukun ganawar ta Ahmed Adamu Mu'azu da masu tunanin sai ta sauyan dai. Sabon yunkurin da ya zo kasa da tsawon mako guda dai tuni ya fara jawo fata a cikin PDP da ta dauki lokaci tana fuskantar rikicin cikin gida.
Wani rikicin ko ni ko kai ne dai ya ruda al'amura a cikin jami'iyyar tare da neman kaita ga ramin kura ga PDP da ta sha alwashin share shekaru har 60 tana fada ana sauraro. Amma kuma ke neman komawa ta adawa a fagen siyasar kasar ta Najeriya.
Abun kuma da yanzu haka ya kai ga fara tsallen murna a cikin gidan na wadata da ke kallon da alamu sabon jagoran na shirin gano baki ga zaren da a fadar Isa Tafida Mafindi dake zaman dan kwamitin kolin jam'iyyar "ya kama hanyar sake farfado da suna da ma kila martabar PDP a idanun kowa".
Sabon fata a cikin gidan wadata ko kuma kokari na janye hankali dai, sabon bazawarin dai na tsakanin dadada wa mai gidansa dake fadar Aso Rock da kuma tuni maitar mulkinsa ta kai ga ko-ina a kasar da kuma tabbatar wa 'yan tawayen fa suna da dama ta rawa dama kila biyan bukatar da ta kai su fada da tsofaffin mamallakan jam'iyyar.
Senator Ibrahim Musa Kazaure dai na zaman daya a cikin 'yan tawayen da suka yi nasarar tabbatar da sabon sauyin, kuma a fadarsa "kawo karshen rikici a cikin jam'iyyar zai ta'allaka ne kawai ga tabbatar da ingantaccen gyara a daukacin harkokin ta".
Tababa ga nasarar dinke baraka cikin PDP
To sai dai koma menene ke iya kai wa ga faranta ran 'yan tawayen dai da kamar wuya kai kawon ta Mu'azu ta kai ga samun nasara ba tare da sake dago da batun karkaba tare da warwareshi domin amfanin kowa ba a cewar Garba Umar Kari wani masani na siyas a kasar.
Yanzu an zura ido a ga nesan siddabarun na Mu'azu ga kokari na shawo kan watsatsen garken PDP da ma raba shanun da danyar ciyawar da suka samu cikin gidan makwabta kyauta.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal