1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kofi Annan zai shiga tsakani a Syriya

February 24, 2012

Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar hadin kan larabawa sun dora wa tsohon jami'in dipolomasiyar Ghana Kofi Annan nauyin sassanta rikicin da ya salwantar da rayukan dubban mutane a Syriya.

https://p.dw.com/p/149Jq
Kofi Annan, Former Secretary-General of the United Nations, takes part in a panel discussion at the University of Ottawa on Friday, Nov. 4, 2011, in Ottawa, Canada. (AP Photo/The Canadian Press, Sean Kilpatrick )
Kofi AnnanHoto: dapd

Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƙungiyar haɗin kan larabawa sun naɗa tsohon sakatare MDD wato Kofi Annan a matsayin mai shiga tsakani a rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a ƙasar Syriya. Manyan hukumomin biyu sun ɗora wa babban jami'in ɗan asali Ghana, nauyin zaƙula hanyoyin kawo ƙarshen zub da jini a Syriya, tare da sasanta ɓangaren shugaba Bashar al-Assad da kuma masu fafutukar tabbatar da demokaradiya a ƙasar.

Wannan naɗin ya zo ne a daidai lokacin da ƙasashen kusan 50 na duniya za su gudanar da wani taro a wannan juma'ar a birnin Tunis na Tuniya, a wani yunƙuri na ci gaba da matsawa al-Assad lamba, da kuma tsara irin agajin gaggawa da za akai wa al'umar ƙasar. Tuni dai ƙasashen rasha da kuma china suka bayyana cewar ba za su halarci wannan taron ba.

A halin yanzu dai, gwamnatin ta Syriya ta na ci gaba da amfani da ƙarfin fiya da ƙima domin karya ƙashin bayan zanga-zangar neman sauyi. Rahotanni sun nunar da cewa mutane kimanin 50 ne dakarun na Syriya suka hallaka a jiya talata ciki kuwa har da fararen hula 43. MDD ta nunar da cewa mutane sama da 6000 ne suka rasa rayukan stun bayan arkewar rikicin Syriya watanni 11 da suka gabata.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu