Kofi Annan ya fara ganawa da mahukuntan Iran a birnin Teheran
September 2, 2006Babban sakataren MDD Kofi Annan ya isa Iran inda yanzu haka yake tattaunawa da hukumomin kasar akan shirin nukiliya na gwamnatin Teheran da kuma halin da ake ciki a Lebanon. Ziyarar ta sa ta zo ne yayin da Amirka ke matsa lamba da a sanyawa Iran takunkumi bayan ta gaza cimma wa´adin kwamitin sulhu na ta dakatar da aikace aikacen inganta sinadarin uranium. Halin da ake ciki a Lebanon zai kasance kan gaba a ziyarar ta mista Annan a daidai lokacin da MDD ke kokarin kara yawan dakarun ta a kudancin kasar. Manufar rangadin sa na kwanaki 10 a yankin na GTT shi ne samun goyon bayan don aiwatar da kudurin kwamitin sulhu wanda ya kawo karshen rikici kwanaki 34 tsakanin Isra´ila da Hisbollah. A jiya juma´a Syria ta yi masa alkawarin girmama haramcin tura makamai ga ´yan Hisbollah.