1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko Ali Abdellah Saleh zai dawo Yemen ?

Sadissou YahouzaJune 6, 2011

Babu alamun cimma zaman lafiya a ƙasar Yemen bayan kwanciyar Ali Abdellah Saleh a asibitin Saudiyya

https://p.dw.com/p/11VOn
Hoto: picture-alliance/dpa

Ƙasashen yammancin duniya sun yi kira ga ɓangarori daban-daban masu yaƙar juna a Yamal sun yi amfani da tafiyar Ali Abdellah Saleh zuwa Saudi Arabiya domin cimma masalaha.

A yayin da ya ke huruci game da batun, ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle cewa yayi:

"Ina fatan fitar Ali Abdellah saleh zuwa Saudiya Arabiya wurin jiyya, zata zama sanadiyar samar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar Yamal.Ina kira da babbar murya ga hukumomin Saudi Arabiyya su yi iya ƙoƙarinsu domin samar da bakin zaren warware wannan rikici da ya ƙi ya ƙi cenyewa".

Duk da cewar shugaban ƙasar Yemen Ali Abdellah Saleh na kwance asibiti, amma ana ci gaba da arangama tsakanin dakarun gwamnati da masu da´awar neman cenji a birane daban-daban na ƙasar.

A wata sanarwar da ya bayyana safiyar yau mataimakin shugaban ƙasar Yemen ya tabbatar da cewar Ali Abdellah Saleh zai dawo Yamal da zaran ya samu sauƙi.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Abdullahi Tanko Bala