Matakan kula da 'yan gudun hijira
July 28, 2021Talla
Filippo Grandi ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake cika shekaru 70 da cimma wannan yarjejeniya ta Geneva kan 'yan gudun hijirar, inda ya ce ya damu matuka ganin yadda wasu kasashe musamman na Turai ke yin watsi da nauyin da ya rataya a wuyansu dangane da batun 'yan gudun hijirar. A cewar Grandi tilas a bi ka'idojin da aka amince da su cikin wannan yarjejniya a duniya baki daya, wajen taimakawa mutanen da ke neman mafaka sakamakon musgunawa da barazana da suke fuskanta a kasashensu na asali. Ya kuma yaba da yarjejeniyar da ya ce, ta taimakawa miliyoyin mutane a duniya.