1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

kisar musulmi a Dogon Dawa na kaduna

October 14, 2012

Mutane akalla 20 sun rasa rayukansu a Dogon Dawa da ke arewacin Najeriya lokacin da 'yan bindiga suka bude musu wuta yayin da suka fitowa daga masallaci.

https://p.dw.com/p/16Pqo
02.10.2012 karte nigeria

Wasu 'yan bindiga sun bude wuta akan wasu musulmi a lokacin da suka fito daga masallaci a garin Dogon Dawa da ke cikin jihar kaduna a arewacin Tarayyar Najeriya. Kimanin Mutane 20 ne dai aka tabbatar cewar sun rigamu gidan gaskiya.

Komishinan 'yan sandan jihar ta Kaduna Olufemi Adenaike ya tabbatar da afkuwar wannan harin a garin da ke kusa da Birnin Gwari. Amma ya ki ya ce uffan game da yawan mutane da suka rasa rayukansu ko kuma suka jikata.

Alhaji Abdulhamid da ya rasa biyu daga cikin 'yayansa a wannan aika aikar ya bayyana wa Deutsche weele cewa tun da karfe biyar ne 'yan bindigan da ke rufe da idanunsu suka afka musu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman