Kiristoci na ci gaba da bukukuwa
April 5, 2015
A cikin sakonsa na bikin Easter da mabiya addinin addinin Kirista ke yi, Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Papa-Roma Francis ya yi tir da tashe-tashen hankula da ake samu musamman harin da aka kai a garin Garissa na kasar Kenya da ya hallaka kusan mutane 150, tare da nuna damuwa bisa rikice-rikicen da ake samu a kasashen Libiya, da Yemen, da Siriya, da Iraki, da Najeriya da wasu sassan na nahiyar Afirka. Ya nuna takaicin yadda ake hallaka mutane domin kawai sun kasance mabiya addinin Kirista.
Sannan Papa-Roma ya yaba da yadda aka amince da yarjejeniyar makamashin nukiliya tsakanin Iran da sauran manyan kasashen duniya. Papa-Roma Francis dan shekaru 78 da haihuwa, ya nuna fata na ganin karshen yadda ake samun rikice-rikicen.