Kiran waya mara haraji a wasu kasashen ECOWAS
March 31, 2017Wadanda ke zama baki a wasu kasashe na Yammacin Afirka za su soma da cin wannan garabasa ta kiran wayarsu a wata kasa. Kasashen da ke karkashin sabon tsarin na "Roaming" sun hada da kasar Senegal da Togo da Saliyo da Cote d'ivoire da Mali da Guinea da Burkina Faso. Wadannan kasashe a tsakaninsu kowa zai iya zuwa kai tsaye cikin wata kasa da layin wayarsa ya yi amfani da shi kaman ya na cikin kasarsa.
Matakin dai an dauke shi ne tun daga watan Yuli na bara a birnin Dakar yayin wani zaman taro na kungiyar hukumomin kula da tafiyar da harkokin sadarwa na Yammacin Afirka. Kuma bisa tsarin da aka yi, matakin zai haifar da samun raguwar kudin kiran waya. Kasar Burkina Faso ita kadai na da masu amfani da wayar sadarwa ta tafi da gidanka miliyan 15. Salimata Mwamba ita ce shugabar hukumar da ke tsari kan harkokin sadarwa ta Burkina Faso ta yi karin haske kan lamarin.
" Mutanen wadan nan kasashe bakwai ba sai sun dauki "SIM card" na kasar da za su ba. Sannan hakan zai bada dama ga mutanen kasashensu su kirasu kai tsaye su samesu idan su na cikin daya daga cikin wadan nan kasashe. Sannan kuma wani abu mai mahimmanci cikin wannan tsari shi ne ba za a cire kudin harajii na kira tsakanin kasa da kasa ba."
Kasashe da dama dai daga cikin kungiyar ta ECOWAS ba sa cikin wannan tsari da wadan nan kasashe bakwai na kungiyar suka yi cikin kasashen da basa ciki har da Jamhuriyar Nijar. Ana iya cewa wadan nan kasashe bakwai daga cikin 15 na ECOWAS da suka rattaba hannu kan wannan tsari har kuma yanzu ya soma aiki, sun shiga a gaban kasashen Turai, inda a cikin kungiyar Tarayyar Turai sai ya zuwa 15 ga watan Yuni ne mai zuwa za a cire kudadan haraji na kiran tsakanin kasashe mambobin kungiyar baki daya.