1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiran Obama ga 'yan Najeriya

Pinado Abdu WabaMarch 23, 2015

Shugaba Barack Obama na Amirka ya yi kira ga 'yan Najeriya da su nisanci tashin hankali a zabukan kasar da za a gudanar a karshen wannan makon

https://p.dw.com/p/1EvqQ
Washington Obama PK
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Obama ya kwatanta zaben a matsayin wata dama ta kafa tarihin da zai kawo cigaba, a kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka. Shugaban ya yi wannan maganan ne sakamakon wasu 'yan rahotannin arangaman da aka samu tsakanin magoya bayan manyan jam'iyyun adawar kasar lokacin da ake yakin neman zabe, kuma fargabar barkewar rikici ya karu sakamakon irin kalaman da wasu daga jam'iyyun na APC da PDP ke amfani da su. Obaman dai ya yi karin bayani kamar haka:

Domin zabe ya kasance mai nagarta wajibi ne a yi zabe na gaskiya ba cuta kuma cikin kwanciyar hankali. Kamata ya yi duk wani dan Najeriya ya kada kuri'arsa ba tare da wata fargaba ko tsoro ba. Shi ya sa na ke kira ga duk shugabani da 'yan takara da su bayyanawa magoya bayansu cewa tashin hankali ba shi da wurin zama a zabe na demokiradiyya, kuma ba zasu zama sanadiyyar shi ba, ba za su taimaka wajen yin shi ba, kuma ba za su yarda a hada kai da su a yi shi ba

Obaman dai ya ce yin zaben cikin nasara da kwanciyar hanakali ne kadai zai taimakawa Najeriyar wajen tinkarar irin kalubalen da ke gabanta yanzu.