1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Rashin karbar tsohon kudi na tarnaki ga kasuwanci

March 10, 2023

Har yanzu 'yan kasuwa na jihohin katsina da Zamfara da ke Arewa maso yammacin Najeriya ba sa amsar tsofaffin kudade duk da umarnin da kotun kolin kasar ta bayar, lamarin da ya sa harkokin kasuwanci ke tafiyar hawainiya.

https://p.dw.com/p/4OWui
Rashin amfani da tsohon kudin Naira na kawa kallo a fannin kasuwanci a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Akasarin 'yan kasuwa na cewa matikar Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai bayar da umarnin ci-gaba da amsar tsofaffin kuddade ba, babu dalilin da zai su amfani da su saboda gudun asara, abin da ya sa har yanzu suke dandana kudarsu, a cewar Jamilu Garba da yake saye da sayarwa a jihar Zamfara.

'Yan kasuwa suka ce ko da sun karbi tsofaffin kuddaden suna tafka asara saboda idan suka je sarin kaya ba'a karba, Kamar yadda wata 'yan kasuwa ta shaidawa DW a babbar kasuwar birnin katsina. Sai dai a cewar shugaban babbar kasuwar birnin katsina Abbas Labaran Albaba, dole ne ke sa 'yan kasuwa suke daukar matakin kin amsar tsofaffin kudade.

Nigeria | Godwin Emefiele und Präsident Muhammadu Buhari | Einführungszeremonie für neu gestaltete Banknoten
Shugaban CBN Emefiele na mika wa Shugaba Muhammadu Buhari sabon kudin NairaHoto: Sodiq Adelakun/Xinhua News Agency/picture alliance

A makon da ya gabata ne kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsofaffin kudaden har zuwa watan Disemba na wannan shakarar. Amma har kawo yanzu ba'aji daga babban bankin Kasar da ma Shugaban kasa kan biyayya da umarnin kotun ba.