1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kim Jong-Un ya ce Trump na da damuwa a cikin kai

Salissou Boukari
September 22, 2017

Jagoran kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya danganta Shugaba Donald Trump na Amirka a matsayin mai damuwa a cikin kwakwalwarsa, inda ya sha alwashin saka Trump din cikin hali na tsaka mai wuya.

https://p.dw.com/p/2kVUY
Nordkorea Diktator Kim Jong-un
Jagoran Koriya ta Arewa Kim Jong-Ung da mayan sojojinsaHoto: Reuters/KCNA

Jagoran kasar Koriya ta Arewa dai ya sha alwashin saka Trump din cikin hali na tsaka mai wuya tunda ya yi barazanar kawar da kasarsa daga doron kasa a gaban Majalisar Dinkin Duniya. A wani bayani da ya yi da kuma kamfanin dillancin labaran kasar na KCNA ya wallafa, Kim Jong-Un, ya ce sai ya sa shugaban Amirka ya biya da tsada kan katobarar da ya yi ta cewa zai kawar da Koriya ta Arewa daga doron kasa. Yayin jawabinsa na farko ne dai a gaban babban zaman taro na Majalisar Dinkin Duniya, shugaban na Amirka ya ce idan har ta kama dole sai Amirka ta kare kanta ko kuma abokan kawancenta daga harin Koriya ta Arewa, to babu wani abun yi illa kawai su shafe Koriya ta Arewa daga doron kasa.

Daga nashi bangare shugaban na Koriya ta Arewa ya soki abun da ya kira tabin kwakwalwa na shugaban da zai yi barazana a gaban Majalisar Dinkin Duniya na kwar da wata kasa mai incin kanta daga doron duniya.