1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kim Jong-Un na son sake ganawa da Trump

Mouhamadou Awal Balarabe
March 1, 2019

Koriya ta Arewa na kokarin farfado da tattaunawar da ke tsakaninta da Amirka bayan da shugabannin kasashen biyu suka kasa cimma matsaya a zaman da suka yi a birnin Hanoi na kasar Vietnam

https://p.dw.com/p/3EK0d
USA-Nordkorea Gipfel - Donald Trump, Kim Jong Un
Hoto: picture-alliance

Korea ta Arewa ta yi tayin sabon zaman tattaunawa da Amirka kwana daya bayan da shugabannin kasashen biyu suka tashi dutse hannu riga a taron kolin da suka gudanar a birnin Hanoi. Hukumomin Pyong Yang suka ce har yanzu kofarsu a bude take kan yunkurin da kasashen duniya ke yi na hana Kim Jong-Un mallakar makamin nukiliya. 

Shugabannin biyu Trump da Kim sun zargi juna da yin karan tsaye a tataunawar da ke zama na biyu da suka gudanar. Shugaba Kim Jong-Un na neman Amirka ta dage wani bangare na takunkuman karya tattalin arzikin da ta aza mata kafin ta mika wuya. Sai dai shugaban Amirka ya jaddada bukatar cika alkawari daga takwaransa na Koriya ta Arewa kamar yadda aka shimfida tun da farko.