Kim da Moon sun kama hanyar daidaitawa
April 27, 2018An yi ta shewa da tayin murna a yayin da shugabanin kasashen Koriya ta Arewa da ta Kudu suka sha hannu a ganawarsu ta farko a shekaru sama da goma. Cike da farin ciki jama’a da dama kama daga Koriya ta Arewa zuwa ta Kudu sun bayyana farin cikinsu na ganin wannan rana da suka ce ba za su taba mancewa da ita ba; da kuma fatan ganin ya kawo karshen rikicin shekaru aru-aru. Ga dukkan alamu dai kasashen biyu sun dauki hanyar sasantawa da juna idan aka yi la’akari da yadda suka shiga zaman na wannan Juma'a suna cike da fara’a da kuma jawabinsu kan mahinmancin zaman nasu. Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jung-un da ya soma jawabi ya yi karin haske kan ganawar tare da fatan biyan bukatar al’ummar da ke jiran jin sakamako na gari daga zaman.
Masana kan harkokin siyasar kasashen biyu sun yaba da matakin da shugaba Kim Jung un na Koriya ta Arewan ya dauka don ganin ya amince da hawa teburin tattaunawa kan rabuwa da makaman nukiliya da ma wasu gwaje-gwaje na makamai masu linzami, batun da ya kasance cikin muhinman batutuwa da ke jan hankulan duniya a baya-bayan nan, kan hadarin kera makaman na kare dangin. A zaman shugaba Kim, cikin raha ya jajanta wa takwaransa kan tashin hankalin da gwaje-gwajensa na makamai da ya ce ya san sun hana shi sukuni.
Shi kuwa a nashi bangaren shugaban Koriyan ta Kudu Moon Jae-in ya jinjina wa takwaran nasa da kuma fatan al’umomin kasashen biyu za su gamsu da ganawar. Da haka ne dai shugabannin kasashen biyu da suka dade suna kai ruwa rana, suka kawo karshen zaman tattaunawar farko kafin su je ga liyafar cin abinci tare da matansu, abin da ake gani a matsayin tafarkin warware rikicin da aka kwashi tsawon shekaru ana yi kenan da kuma kawar da fargabar barkewar yakin duniya mafi muni.