1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Khamenei ya bukaci fitowar masu zabe

Suleiman Babayo MA
July 3, 2024

Shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bukaci 'yan kasar su yi dafifi wajen fitowa kada kuri'a a zaben shugaban kasa zagaye na biyu ranar Jumma'a mai zuwa.

https://p.dw.com/p/4hpNI
Iran | Zabe
Shugaban addinin Iran Ayatollah Ali KhameneiHoto: Office of the Iranian Supreme Leader/WANA/REUTERS

Ayatollah Ali Khamenei, shugaban addinin na kasar Iran, ya bukaci al'umar kasar kan fitowa ranar Jumma'a mai zuwa domin kada kuri'a a zaben shugaban kasa zagaye na biyu da za a gudanar tsakanin mai rajin kawo sauyi Masoud Pezeshkian, da kuma mai tsattsauran ra'ayi da kin jinin kasashen yamma Saeed Jalili.

'Yan kasar miliyan 61 sukake da damar kada kuri'a, domin zabar sabon shugaban kasa, wanda zai maye gurbin marigayi Ebrahim Raisi da ya rasu sakamakon hatsarin jirgi mai saukar ungulu a watan Mayu na wannan shekara ta 2024.

A zagaye na farko na zaben na ranar 28 ga watan jiya na Yuni dai Masoud Pezeshkian ya samu kashi 42 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da Saeed Jalili ya samu kashi 38 cikin 100. Karkashin tsarin kasra ta Iran ana bukatar dan takara ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 domin kaucewa zuwa gazaye na biyu na zabe.