Kaduna: Kare masu bukata ta musamman
May 26, 2021Kungiyar kare hakkin Nakasassun Najeriyar wato "Beyound the Border of Disability," ta nunara da cewa sayan kayan zai taimaka wajen kera kayayyakin da ke wuce kyan na kasashen katare, wanda kuma zai taimaka musu wajen bankwana da barace-barace a gefan hanya. Masu bukata ta musamman da mafi yawansu guragu ne, sun rungumi hanyar anfani da hikimomi da fasaharsu wajen kama sana'ar ta kere-keren kofofin gidaje na zamani da aikin walda da harhada wasu kayayyakin motoci.
Sai dai babban kalubalen da suke fuskanta shi ne na yadda ake nuna musu kyama ta hanyar gujewa sayen kayan da suka kera, lamarin da ke kashe masu kwarin guwiwa. Kwarade Rilwanu Abdullahi shi ne shugaban kungiyar guragun Najeriya, ya kuma nuna takaicinsa bisa ga yadda al'ummar ke kyamatar kayayyakinsu, inda ya yi kira kan daina kyamar kayayyakin mutane masu bukata ta musamman ganin cewa suma suna da baiwa da hikimar da kowane dan Adam ke da ita fadin duniya. A cewar kwararru masana zamantakewa a Najeriyar, akwai bukatar gwamnati ta kara bullo da hanyoyin karfafa masu bukata ta musamman, dan ganin sun rungumi kananan sana'o'in hannu da zumar kaucewa zama a gefan titi.